Sakamakon da hukumar ta fara fitarwa a ranar Talata na nuna cewa shugaba Mahamadou Issoufou ne ke kan gaba.
'Yan adawar sun bayyana kin amincewarsu ne a yayin wani taron manema labarai da suka kira a Yamai.
Jam'iyyun sun zargi PNDS Tarayya mai mulki da hada baki da hukumar zabe, wajen bayyana sakamakon da suka ce ba na gaskiya ba ne.
Sun kuma yi zargin cewa akwai manyan rumfunan zabe na bogi da aka kada kuri'a a kasar.
Hukumar zaben da kuma jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki duka sun musanta zarge-zargen.288